
Wata mata me suna Refilwe Motiang ‘yar kasar Afrika ta Kudu ta sha da kyar bayan da ta je gyaran gira.
Refilwe data fito daga yankin Midrand na birnin Johannesburg, tace zata yi tafiyane shine ta je a mata gyaran gira dan ta kara kyau.
Matar tace ta je ta zauna an fara mata gyara sai ta ji tana jin zafi.
Tace anan ta gayawa me mata gyaran girar amma sai tace mata hakan ba matsala bace gam din ne me karfi ne.
Saidai tace can taji zafin yayi yawa ba zata iya jurewa ba.
Tace haka ta tashi tsaye ta fita.
Tace anan ta ji da kyar take bude idonta, da gudu aka garzaya da ita zuwa Asibiti.
An dan kwantar da ita aka bata magani amma daga baya aka sallameta, yanzu tana jin sauki.
Matar tace ta yi nadamar yunkurin yin gyaran girar inda tace tana tunanin kar me shagin gyaran kara saboda sakaci