
Wannan fa cìn mutuncin ne ga ilahirin mutanen Arewa ne ba kawai Kano ba. Hatta sarautar gargajiya na ilahirin Arewa a nawa hangen!
Duk dama ‘ýan sanda suna da damar gayyatan kowaye a Nijeriya idan dai har ana tuhumar shi da wani laifi amma ya kamata a yi abu cikin adalci da kuma mutunci.
Wasu za su yi murna, amma wannan abunda IGP ya keyi cin mutunci ne ga Sarautar Gargajiyarmu.
Don haka ina mai rokon shugaban ‘yan sanda na kasa da ya sake yin duba da wannan wasikar gayyatar, ya kuma samo wata hanya ta magance wanna matsala.