Friday, December 5
Shadow

Gòbàrà ta làlàtà dukiya a kasuwar Kara a Birnin Kebbi

Wata mummunar gobara da tashi a kasuwar Kara a Birnin Kebbi, ta lalata shaguna da kuma dukiyoyi da dama.

Gobarar wadda ta soma a safiyar yau Lahadi, ta janyo asarar kayayyaki da kuɗinsu ya kai na miliyoyin naira.

Wasu shaidu sun bayyana cewa wutar ta yaɗu da sauri kafin a samu zuwan masu kashe gobara, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

“Mun ga hayaki na tashi ko ta ina, nan da nan wutar ta karaɗe yawancin shaguna da ke cikin wannan kasuwa,” in ji wani ɗan kasuwa mai suna Musa Bello.

Ba a samu rahoton asarar rai ba a gobarar, sannan zuwa yanzu ba a san abin da ya haddasa ta ba.

Karanta Wannan  Wallahi idan Jam'iyyar su Atiku ta karbi mulki sai kun ce gara Tinubu dasu>>Sheikh Musa Asadussunnah

Gwamnatin jihar Kebbi ta jajantawa waɗanda lamarin ya shafa a wata sanarwa da ta fitar.

Ta nuna takaicinta kan afkuwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *