Sunday, August 9
Shadow

Gwamnatin jihar Kano ta nemi gwamnatin Tarayya ta biyata diyya saboda hana hawan sallah tsawon shekaru 2

Gwamnatin jihar Kano ta nemi Gwamnatin tarayya ta biyata diyya saboda hana hawan Sallah na tsawon shekaru 2.

Kwamishinan kananan hukumomi da sarautun gargajiya, Alhaji Tajo Uthman ya bayyana haka a yayin da me martaba, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya kaiwa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Ziyara a gidan Gwamnatin Jihar.

Ya bayyana cewa, wannan hani yasa sun tafka babbar asara saboda mutane daga ciki da wajen Najeriya na zuwa kallon hawan Sallar.

Ya bayyana cewa, Har majalisar Dinkin Duniya ta san da zaman hawan Sallar a Kano kuma rashin kudin da suke samu daga hawan Sallar ya taba kasafin kudin jihar.

Karanta Wannan  An koma International Kalli Bidiyon: 'Yan kasar waje Fararen fata sun fara dora hoton Adam A. Zango suna nuna masa kauna bayan da Hadiza Gabon ta ki saka Hotonsa a dakin da take hira da mutane

Ya bayyana cewa, Dan haka gwamnatin tarayya ta biya musu kudaden da suka rasa na hawan Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *