
Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa, Gobara ta tashi a makarantar Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake Rafin Albasa a jihar.
Rahoton Daily Trust yace Gobarar ta cinye ginin wanda benene inda ta lalata kayan aiki dake ofis-ofis na cikin ginin.
Zuwa yanzu dai ba’a gano dalilin faruwar Gobarar ba.
Shugaban Gidauniyar Dahiru Bauchi, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru ya jajantawa dalibai da malaman makarantar kan wannan ibtila’i.
Yace sun godewa Allah da ba’a samu asarar rai ba.
Yace Sheikh Dahiru Bauchi ne ya kafa makarantar inda Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya budeta.
Yacw an yi asarar litattafai na malam da na marigayi Sheikh Hadi Dahiru Bauchi, dana Ahmad Sheikh Dahiru da sauransu.
Yace gobarar ta tashine bayan an tashi daga makarantar.