
Gwamnatin tarayya ta sanar da ciwo bashin Dala $747m dan gina Titin Legas zuwa Calabar.
Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana hakan.
Yace za’a yi amfani da kudi ne wajan gina sashen farko na titin wanda ya tashi daga Victoria Island zuwa kauyen Eleko.
Yace aikin zai jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje.