
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya sakawa sabuwar gadar sama da ya gina sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Sule ya bayyana hakane yayin bude gadar a ranar Laraba.
Yace tsarin Gwamnatin Tinubu ne ya karfafa masa gwiwar aikata wannan aiki inda yace kuma an yi wadannan ayyukane ba tare da cin bashi ba.