
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da rashawa ta Kano, Barista Sa’idu Yahaya.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a fadar gwamnatin Kano ranar Laraba, inda Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi, ya jagoranci ɗaukar rantsuwar aiki.
A ranar 1 ga watan Agusta, Gwamna Yusuf ya gabatar da sunan Barista Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar, sannan aka tura sunan nasa zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatarwa. Wannan nazuwa ne bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado.
An haifi Yahaya a shekarar 1978, kuma ƙwararre ne a fannin yaƙi da cin hanci. Yana da digiri a tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano (BUK) da kuma digirin digirgir (MBA) a harkar kasuwanci, inda ya kware a sha’anin ƙirƙirar sana’o’i da zuba jari.
Yahaya na da gogewa fiye da shekaru 18 a Hukumar Yaƙi da Cin Hanci ta (ICPC), inda ya riƙe muhimman mukamai ciki har da jagorantar sashen bincike da bibiyar ayyukan ‘yan majalisa.