
Gwamnan jihar Borno a arewacin Najeriya, Babagana Zulum, ya amince da bai wa iyaye maza N250,000 da iyaye mata N50,000 na ɗalibai 90 a garin Gajiganna da ke jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake ƙaddamar da makarantar Islamiyya ta Higher Islamic College Gajiganna, inda ya yi alƙawarin ciyar da ɗaliban kyauta a kullum.
“Za mu bai wa kowane uba N250,000, da kowace uwa N50,000. Kowane ɗalibi kuma zai samu N50,000 domin biyan buƙatunsa,” in ji wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar.
Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin ne domin ƙarfafa wa iyaye gwiwa wajen kai yaransu makarantar da ke arewacin Borno, yankin da yaƙin Boko Haram ya ɗaiɗaita.
Gajiganna mai mutane kimanin 50,000, ɗalibai 90 ne kacal ke zuwa makaranta a garin, a cewar Gwamna Zulum.
“Dole ne mu tabbata waɗannan ɗalibai 90 sun kammala karatunsu. Nasararsu za ta zama babban zakaran gwajin dafi a ɓangaren cigaban ilimi a arewacin Borno,” kamar yadda ya bayyana.