Friday, December 5
Shadow

Gwamnan Benue ya tona Asirin masu daukar nauyin hàrè-hàrèn ‘yan tà’àddà

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya zargi wasu ƴan siyasa da ke ci a majalisar tarayya da ɗaukar nauyin hare-hare da ake kai wa jihar, inda ya ce ba za su lamunci hakan ba.

Gwamnan ya yi wannan zargi ne yayin tattaunawa a shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels.

Duk da cewa bai bayyana sunayen ƴan siyasar ba, gwamnan ya ce kwamitin da ya naɗa domin yin binciken kan batun kai hare-haren ya gano akwai sunayen manyan ƴan siyasa, inda ya sha alwashin ɗaukar mataki nan take idan ya karɓi rahoton kwamitin a mako mai zuwa.

“Abin takaici yadda wasu manyan ƴan siyasa ke ci gaba da bai wa ƴan bindigar da ke kai hare-haren mafaka da kuma saya musu makamai. Za mu ɗauki mataki tun da ba su damu da irin rayuka da suke salwantar wa ba,” in ji gwamna Alia.

Karanta Wannan  Majalisar Tarayya zata yi dokar tilasta Amfani da motoci masu amfani da wutar Lantarki kadai

Jihar ta Benue dai na fama da ƙaruwar hare-hare a ƴan makonnin nan, inda ƙananan hukumomi da dama da ke fuskantar mummunan tashin hankali da ya janyo asarar rayuka da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *