Friday, April 11
Shadow

Gwamnan jihar Kebbi ya dakatar da hadiminsa saboda yace jihar ta Kebbi na kan gaba wajan yawan ‘yan Lùwàdì da Màdìgò

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya dakatar da babban sakatare a gwamnatinsa, Nasiru Abubakar Kigo saboda ikirarin da yayi cewa, jihohin Sokoto da Kebbi ne suka fi yawan ‘yan Luwadi da Madigo.

Sakataren yada labarai na jihar, Ahmed Idris ne ya tabbatar da dakatar da Nasiru Abubakar Kigo a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa, tuni shugaban ma’aikata na jihar, Malami Shekare ya baiwa Nasiru Abubakar Kigo takardar dakatarwar da aka masa.

Takardar tace an dakatar dashine saboda ikirarinsa na cewa, jihar Kebbi na kan gaba wajan yawan ‘yan Lùwàdì da Màdìgò wanda hakan ya kawo rudani da batawa jihar suna.

Karanta Wannan  Allah Sarki: 'Yar Bautar kasarnan, Rofiat Lawal da aka yi gàrkùwà da ita ta shaki iskar 'yanci bayan da danginta suka biya kudin Fànsà Naira Miliyan 1.1

Gwamnatin jihar ta musanta ikirarin na Kigo inda ta bayyanashi a matsayin mara tushe.

Kigo wanda kuma malamin addinine yayi wannan ikirarin ne a rukunin gidajen Adamu Aliero dake jihar Kebbi yayin wata bita a lokacin Azumin watan Ramadana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *