Wednesday, March 18
Shadow

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da ƙarin dakarun tsaro na jihar

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da ƙarin dakarun tsaro na jihar.

Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ƙaddamar da sabbin rukunin jami’an tsaro na da ake kira KTS C-Watch.

Dakarun tsaron unguwannin 550 su ne kashi na biyu da Gwamna Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar a yau Juma’a da zimmar yaƙi da ‘yanfashin daji masu sacewa da kashe mutane haka kawai.

“Mun ɗauki mutum 6,652 domin daƙile matsalar tsaro. Sannan mun nemi masu gari, da limamai, da ladanai, tare da ba su albashi a matsayin wani ɓangare na shirin samar da tsaro a unguwanni,” a cewar gwamnan.

Karanta Wannan  A yayin da yake sukar Gwamnatin Muslim Muslim, an gano cewa Rev. Ezekiel Dachomo na daga cikin wadanda matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta rabawa kudade a jihar Filato

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *