Friday, December 5
Shadow

Gwamnan Katsina ya tafi hutu don kula da lafiyarsa

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya sanar da tafiya hutun mako uku don kula da lafiyarsa.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango ya fitar, ya ce gwamnan zai fara hutun ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agustan 2025.

“Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi aiki cikin yanayi mai kyau, na ɗauki wannan matakin tafiya hutu, kuma zan dawo da zarar likitoci sun gama duba ni,” in ji Gwamna Radda.

Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Malam Faruk Jobe.

A watan Yuli ne gwamna Radda ya yi hatsarin mota a kan hanyar Katsina zuwa Daura.

Karanta Wannan  Hotuna: An Gudanar Da Jana'izar Ga'ib Ga Marigayi Aminu Dantata A Kano, Manyan mutane sun halarta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *