Aliko Dangote ya bayyana cewa,Farashin man fetur da zai rika sayarwa daga matatarsa gwamnatin tarayya ce zata kayyade farashinsa.
Yace majalisar zartaswa ce zata kayyade farashin man kuma yace au ta bangarensu abinda suke jira kenan.
Dangote kuma yace mansa na da ingancin da zai yi gogayya da na kowace kasa a Duniya.