Sunday, December 14
Shadow

Gwamnati ta bayyana jihohin da suka fi fama da tsadar kayan Abinci a Najeriya, Duba kaga jiharka na ciki?

Hukumar NBS dake kula da kididdigar alkaluma a Najeriya ta fitar da bayanan Alkaluma kasuwanci da kayan Masarufi na watan maris.

Hukumar tace alkaluma sun nuna makin farashin kayan masarufi ya tsaya a mataki na kaso 23.71 cikin 100.

Hakan na nufin farashin kaya masarufi sun yo kasa idan aka hada da alkaluma baya da aka samu.

Saidai Jihohin Enugu, Kebbi, Niger, Benue, Ekiti, Nassarawa, Zamfara, Delta, Gombe, Sokoto, da babban birnin tarayya Abuja, nasu Alkaluman sama suka yi.

Rahoton yace wadannan jihohi alkaluansu sun nuna suna da maki 30 cikin 100 na hauhawar farashin kayan masarufi.

Karanta Wannan  An yi jana'izar mutanen da harin jirgi ya kashe bisa kuskure a Zamfara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *