
Tsohon shugaban jam’iyyar Hadakata ta ADC, Ralph Nwosu ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta masa tayin mukamin Minista har sau 3 dan ya bar jam’iyyar amma yaki.
Ya bayyana hakane a ranar Talata a yayin da aka mikawa David Mark shugabancin jam’iyyar a hukumance.
Yace kokarin na gwamnati yana son dakile kaifin duk wasu ‘yan adawa ne dan mayar da Najeriya tsarin tafarkin jam’iyya daya.
Yace an masa tayin kujerar Minista guda 3 ne dan ya dauki daya yayi kyauta da guda 2. Saidai yace ya zabi Dimokradiyyar Najeriya da ci gabanta.
Ya kara da cewa, Najeriya ba zata zama kasa me jam’iyya daya ba bayan kokarin da aka yi na ganin an kawar da tsarin mulkin kama karya na soja.
Yace tun bayan bayyana hadakatar ‘yan Adawa a jam’iyyar ta ADC membobin jam’iyyar sun karu zuwa mutane Miliyan 3.
Yace yanzu suna da sanatoci 28 sannan suna da ‘yan majalisar wakilai 60