
Gwamnatin tarayya ta wallafa hotunan masu laifi da suka tsere daga gidan gyara hali na Ilesa dake jihar Osun.
Gwamnatin tace ta saka ladar Naira Miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka aka kama su.
Da safiyar ranar Talata ne dai masu laifin suka tsere a yayin da ake tsaka da ruwan sama.
