Monday, December 16
Shadow

‘Gwamnati za ta ci gaba da biyan ma’aikata ƙarin albashin wucin gadi’

Gwmanatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da bai wa ma’aikatan ƙasar ƙarin albashin wucin gadi – da ta fara biya wata shida ta suka gabata – har zuwa lokacin da za a kammala cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.

Cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai ranar Asabar a Abuja, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce wa’adin mafi ƙarancin albashi da aka yi a shekarar 2019 ya ƙare ne ranar, 8 ga watan Afrilun 2024.

Sai dai ministan bai bayyana adadin kuɗin da gwamnatin ke biya a matsayin albashin wucin gadin ba, to a baya gwamnatin ta ce za ta riƙa biyan ma’aikatan ƙarin naira 35,000 a kan albashinsu kowane wata har na tsawon wata shida.

Karanta Wannan  Kuma Dai: Kungiyar Kwadago, NLC tace zata iya amincewa idan gwamnati ta biya kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) a matsayin mafi karancin Albashi

A ranar juma’a ne dai ƙungiyoyin ƙwadogon ƙasar suka ce za su tsunduma yajin aiki daga gobe Litinin, kasancewar wa’adin ranar 31 ga watan Mayu da suka bai wa gwamnati na amincewa da mafi ƙarancin albashi ya wuce ba tare da cimma matsaya ba.

Gwamnatin ta ce amince da biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙasar, to amma haɗakar ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun yi watsi da wannan ƙari, inda suka buƙaci gwamnati ta biya raira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai shugaban ƙasar ya yi wata ganawa da jagororin gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon bayan da suka yi barazanar shiga yajin aiki kan matakin shugaban na cire tallafin man fetur.

Karanta Wannan  Hotunan Yadda Matashiyar Farfesa Aisha Sani Maikudi, Yar Asalin Jihar Katsina Ta Karbi Ragamar Shugabancin Jami'ar Abuja, Yau Litinin

A lokacin ganawar shugaba Tinubu ya yi musu alƙawura da dama ciki har da amincewa da ƙarin albashin wucin gadi na Naira 35,000 ga kowane ma’aikaci, har tsawon wata shida, kafin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi.

Kan haka ne ministan yaɗa labaran ya ce kasancewar har yanzu ba a kammala cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin ba, gwamnati za ta ci gaba da bayar da wannan ƙari har zuwa lokacin da za a cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin.

”Alƙwarin gwamnatin tarayya na yi wa ma’aikata ƙari a albashinsu na wata shida, ba zai dakata ba har sai an kammala cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi”, in ji ministan

Karanta Wannan  Tsadar rayuwa: Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce sai da suka yi wa 'yan Nijeriya gargadi kar su sake yin kuskuren zaben jam'iyyar APC a zaben 2023

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta ɓullo da wannan tallafi ga ma’aikatan ƙasar ne domin tabbatar da cewa ba su galabaita ba, kafin cimma matsaya a kan mafi ƙarancin albashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *