Gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewa za ta rage wa manoman da suka sha fama da hare-haren Boko Haram kuɗin mai domin rage musu raɗaɗi.
Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da haka a ranar Juma’a a garin Bama yayin rabon tallafin kayan aikin gona ga manoma sama da 5,000 waɗanda hare-haren Boko Haram ya ɗaiɗaita.
A cewar gwamnan, za a rage kuɗin litar mai wanda ake sayarwa kan naira 1,000 da kuma 1,200 a Maiduguri zuwa 600 ga manoman.
“Mun yi haka ne da zimmar rage wa manoman raɗaɗi ko kuma matsalolin kuɗi da suke fuskanta, musamman ma a yankuna da aka lalata wa gine-gine da kuma wuraren kasuwanci sakamakon rikicin Boko Haram na tsawon shekaru,” in ji Zulum.