
Gwamnatin jihar Kano ta nemi Gwamnatin tarayya ta biyata diyya saboda hana hawan Sallah na tsawon shekaru 2.
Kwamishinan kananan hukumomi da sarautun gargajiya, Alhaji Tajo Uthman ya bayyana haka a yayin da me martaba, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya kaiwa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Ziyara a gidan Gwamnatin Jihar.
Ya bayyana cewa, wannan hani yasa sun tafka babbar asara saboda mutane daga ciki da wajen Najeriya na zuwa kallon hawan Sallar.
Ya bayyana cewa, Har majalisar Dinkin Duniya ta san da zaman hawan Sallar a Kano kuma rashin kudin da suke samu daga hawan Sallar ya taba kasafin kudin jihar.
Ya bayyana cewa, Dan haka gwamnatin tarayya ta biya musu kudaden da suka rasa na hawan Sallah.