
Gwamnatin jihar Lagos ta nada Mandy Kiss, Matashiyarnan data yi yunkurin shiga kundin Tarihin Duniya ta hanyar yin lalata da maza 100 jakadiyar yaki da miyagun kwayoyi.
Lamarin ya baiwa mutane mamaki matuka lura da irin hanyar data dauka ta badala amma hukumomi suka bata aikin jakadanci.
A baya dai, Hukumar hana sha da fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ta baiwa shahararren mawakinnan kuma mashayi, Naira Marley jakadan yaki da ta’ammuli da miyagun Kwayoyi.
Da take martani kan wannan jakadanci data samu, Tace a baya da take magana a matsayin mutuniyar kirki babu wanda ya kulata amma yanzu da ta dau hanyar badala gashi har ta zama jakadiya.