
Gwamnatin Kano Ta Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye a Kafafen Watsa Labarai
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana dakatarwa nan take ga dukkan shirye-shiryen siyasa da ake yadawa kai tsaye a kafafen watsa labarai na jihar.
An bayyana wannan mataki ne yayin taron tattaunawa na kowane lokaci da ake gudanarwa a Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, wanda Kwamishinan Yada Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranta tare da shugabannin kafafen yada labarai.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Harkokin Musamman na ma’aikatar, Sani Abba Yola, ya sanyawa hannu, an dauki wannan mataki ne don dakile yada kalaman da za su iya haifar da fitina da barazana ga zaman lafiya da daidaiton al’adu da addini a jihar.
“Ba mu dauki wannan mataki don murkushe ‘yan adawa ba,” in ji Kwamared Waiya. “Manufarmu ita ce kare mutuncin al’adunmu da dabi’un addini na jihar Kano.”
An kuma yanke wasu sabbin matakai yayin taron, ciki har da bukatar duk wanda zai bayyana a shirin kafar yada labarai ya rattaba hannu kan alkawarin kauce wa kalaman batanci, zagi, da cin zarafin al’ada ko addini.
An umarci masu gabatar da shirye-shirye da su guji tambayoyi ko alamu da ka iya janyo kalaman batanci ko shafar mutuncin wasu ko martabar jihar.
Kwamared Waiya ya ce an samu raguwar amfani da kalaman batanci a shirye-shiryen rediyo da talabijin, yana mai danganta hakan da ci gaba da tuntuba tsakanin gwamnati da kafafen watsa labarai.
Ya kara da cewa gwamnati ta kaddamar da shirin wayar da kai ga masu gabatar da shirye-shiryen siyasa, masu sharhi a kafafen yada labarai, da kuma membobin Majalisar Limaman Juma’a.
“Muna son tabbatar da cewa sakonni na siyasa suna zuwa cikin yanayi mai mutunci, ba tare da batanci ko cin mutunci da zai iya bata sunan jiharmu ba,” in ji shi.