
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya yi watsi da gargaɗin Shugaba Trump na ɗaukar matakin soji kan Najeriya.
Yayin da yake jawabi a taron manema labarai da ya gudanar a birnin Berlin tare da takwaransa na Jamus, Mista Tuggar ya ce Najeriya na bayar da ƴancin addini tare da aiki bisa doron doka.
”Kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin ƙasar sun haramta cin zarafin addini tare da bayar da damar ƴancin gudanar da addini”, in ji shi.
”Babu yadda za a yi gwamnatin Najeriya ta goyi bayan ta kowane fanni na yadda za a ci zarafin mabiya wani addini”, in ji Tuggar.
Ministan harkokin wajen na Najeriya gwamnatin ƙasar ba za ta yarda a mayar da ƙasar tamkar Sudan ba.
”Abin da muke so duniya ta fahimta shi ne ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin, Najeriya na da yawan al’umma fiye da miliyan 230, ƙasar da ta fi kowace yawan jama’a da ƙarfin dimokraɗiyya a Afirka”, a cewarsa.
Ya ƙara da cewa an ga yadda ƙasar Sudan ta koma sakamakon rikici mai alaƙa da addini da ƙabilanci da kuma ɓangaranci.
”Don haka babu wanda ya kamata ya magance matsalolin Afirka sai mu ƴan Afirka, kamar Najeriya – wadda ke a matsayin mamba a kwamitin tsaro na ƙungiyar Tarayar Afirka.