
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta ce ta kori wasu jami’anta 115 daga aiki, saboda abin da ta kira wasu sauye-sauye da hukumar ke yi.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, a ranar Talata, DSS ta shawarci al’umma su kauce wa mu’amala da jami’an a matsayin wakilan hukumar.
Hukumar ta kuma wallafa sunaye da hotonan jami’an 115 da ta ce ta koran a shafinta intanet.
Bayanan mutanen da hukumar ta fitar sun nuna cewa an kori mutanen ne tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025.
Matakin na zuwa ne bayan da a watan Oktoban da ya gabata hukumar ta kama wasu tsoffin jami’anta biyu bisa zargin amfani sa sunan hukumar suna damfarar mutane.