Thursday, January 16
Shadow

Gwamnatin Najeriya za ta fara yi wa mata tiyatar haihuwa kyauta

Ma’aikatar lafiya a Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri na yi wa mata masu ciki tiyata kyauta a faɗin ƙasar.

Shirin da aka yi wa take da Maternal Motality Reduction Innovation Initiative Mamii), an ƙaddamar da shi yayin wani taron bita na shekara-shekara a Abuja.

Ministan Lafiya Muhammad Ali Pate ya bayyana shirin da zimmar rage mutuwar mata yayin haihuwa a faɗin Najeriya.

“Babbar manufar wannan shiri ita ce yi wwa mata marasa ƙarfi tiyatar haihuwa kyauta, amma waɗanda suka cika ƙa’ida a asibitocin gwamnati da na kuɗi,” a cewar ministan.

“Ta hanyar cire matsalolin kuɗi, muna ganin babu wata mace da ya kamata a bari ba tare da an kula da ita ba ko da ba ta da kuɗi.”

Karanta Wannan  Adawa tsakanin tsofaffin gwamnoni na mayar da Kano baya - Garo

Ya ƙara da cewa mutuwa yayin haihuwa na ci gaba da zama barazana, inda ƙananan hukumomi 172 ke haifar da kashi 50 cikin 100 na dukkan mace-macen da ake samu wajen haihuwa a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *