Friday, December 6
Shadow

Abubuwa bakwai da Trump ya ce zai yi a matsayin shugaban Amurka

Donald Trump na kan hanyar komawa fadar White House bayan da ya alƙawarta kawo ƙarshen wasu matsaloli ciki har da batun ‘yan cirani, da tattalin arziki, da yaƙin Ukraine.

Da alama ya samu ɗimbin magoya baya sakamakon manufofinsa na siyasa, musamman a majalisar dokokin ƙasar bayan da jam’iyyarsa ta Republican ta sake ƙwace iko da majalisar dattawan ƙasar.

A jawabin murnar lashe zaɓe da ya gabatar, Mista Trump ya sha alwashin ”yin mulkin bisa taken: ‘Cika alƙawuran da muka ɗauka’.

Amma a wasu fannonin, ya bayar da taƙaitaccen bayanin yadda zai cimma manufofin nasa.

A lokacin da kafar yaɗa labarai ta Fox News ta tambaye shi a 2023, ko zai yi amfani da kujerarsa ta hanyar da ba ta dace ba, ko muzguna wa ‘yan adawar siyasa? Sai ya ce ba zai yi ba, ”in ban da a ranar farko”.

“A,a ba zan yi hakan ba, in ka cire ranar farko. Za mu rufe kan iyaka, kuma muna bincikowa, za kuma mu ci gaba da bincikowa, daga nan kuma shikenan, ba zan ƙara zama ɗan kama-karya ba.”

1. Korar baƙin haure marasa takardun izini

Yayin da yake gudanar da yain neman zaɓensa, Trump ya alƙawarta gagarumin korar baƙi a tarihin ƙasar na marasa takardun izinin zama Amurka.

Ya kuma alƙawarta kammala aikin ginin katanga tsakanin Amurka da Mexico da aka faro lokacin wa’adin mulkinsa na farko.

A ƙarshen shekarar 2023 ne adadin baƙin hauren da ke kwarara cikin ƙasar ya kai matakin da ba a taɓa gani ba, kafin ya fara raguwa a 2024.

Masana sun shaida wa BBC cewa wannan alƙawari na korar baƙi da Trump ya yi, zai fuskanci turjiya daga ɓangaren shari’a, kuma hakan zai haifar da jan ƙafa kan haɓakar tattalin arzikin ƙasar.

Karanta Wannan  ƊAN DUNIYA: An kori mutumin da ake zargi da keta haddin matan aure kusan 400 a kasar Equatorial Guinea daga aiki

2. Matakan tattalin arziki da haraji

Ƙuri’ar jin ra’ayi ta nuna cewa tattalin arziki na ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da masu zaɓe suka yi la’akari da su.

Trump ya alƙawarta kawo ”ƙarshen hauhawar farashi” – wadda ta kai matakin ƙoƙoluwa a gwamnatin Biden kafin ta fara raguwa. To amma ikon shugaban ƙasa na rage hauhawar farashi takaitacce ne.

Ya kuma alƙawarta rage kuɗin haraji, inda zai ɗora kan shirin haraji na 2017 da ya faro. Ya yi yunkurin cire haraji kan wasu abubuwan tare da soke shi kan abubuwan da suka shafi harkokin rayuwa da tsaro.

Mista Trump ya kuma ƙuduri aniyar sanya sabon haraji na aƙalla kashi 10 kan kayyakin waje, domin rage giɓin kasuwanci. Kakkayakin da aka shigar kasar daga China za su fuskancin ƙarin kashi 60 na haraji, kamar yadda ya ce.

Masana tattalin arziki sun yi gargaɗin cewar hakan zai ƙara farashi, musamman ga talakawa.

3. Soke dokokin sauyin yanayi

A lokacin wa’adin mulkinsa na farko, Trump ya yi watsi da ɗaruruwan yarjejeniyoyin kare muhalli, sannan ya sa Amurka ta kasance ƙasa ta farko da ta fice daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta ‘Paris climate agreement’.

A wannan karon, ya sake shan alwashin soke wasu dokokin, musamman ta yadda zai taimaki masana’antun ƙera ƙananan motoci.

Ya sha sukar motoci masu amfani da lantarki, inda ya alƙawarta soke ƙudirin Biden na komawa amfani da motocin da ba sa gurɓata muhalli.

Ya kuma alƙawarta ƙara samar da man fetur a Amurka, inda ya sha alwashin ”tona, da ƙara tona da sake tono” don taimaka wa wasu fannoni, kamar samar da makamshi ta hanyar iska.

Karanta Wannan  Hotuna:Sau 3 wadannan iyayen na haihuwar jarirai suna yaddawa

Yana kuma son buɗe wuraren samar da makamashi kama daga tono mai zuwa na iska, wanda ya ce hakan zai taimaka wajen rage farashin makamshi a ƙasar, kodayake masu sharhi na nuna shakku kan batun.

4. Kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

Trump ya sha sukar kashe biliyotn daloli da Amurka ke yi wajen goyon bayan yaƙin da Ukraine ke yi da Rasha, sanna kuma ya alƙawarta kawo ƙarshen yaƙin ”cikin sa’o’i 24” ta hanyar sulhu.

Bai bayyana abin da yake tunanin kowane ɓangare zai haƙura shi ba. Jam’iyyar Democrats ta ce matakin zai ƙarfafa wa Shugaba Vladimir Putin gwiwa.

Trump na son Amurka ta nesanta kanta daga duka yaƙe-yaƙen da ake yi a ƙasashen waje.

Dangane da yaƙin Gaza, Trump ya ayyana kansa a matsayin cikakken magoyin bayan Isra’ila, to amma ya buƙaci ƙawar Amurkan ta kawo ƙarshen hare-harenta.

Ya kuma alƙawarta kawo ƙarshen yaƙin Lebanon, amma bai yi cikakken bayanin yadda zai aiwatar da hakan ba.

5. Babu haramcin zubar da ciki

Saɓanin muradun wasu magoya bayansa, Trump ya faɗa a lokacin muhawararsa da Kamala Harris cewa ba zai sanya hannu kan dokar haramcin zubar da ciki ba.

A 2022, Kotun ƙolin ƙasar – wadda mafi yawan alƙatanta masu ra’ayin riƙau ne da Trump ya naɗa a wa’adinsa na farko – ta soke ‘yancin zubar da ciki.

‘Yancin zubar da ciki ya kasance wani babban al’amari a yaƙin neman zaɓen Harris, kuma yawancin jihohi ƙasar sun amince da dokokin haramcin zubar da ciki a zaɓen.

Karanta Wannan  Tsaka Mai wuya: Da wuya Osimhen ya bugawa Napoli wasa a wannan shekarar

Trump da kansa ya sha faɗin cewa jihohi na da damar aiwatar da dokokinsu kan zubar da ciki.

6. Afuwa ga masu boren 6 ga watan Janairu

Trump ya ce zai “saki” wasu da aka samu da laifi a lokacin wani bore a birnin Washington DC ranar 6 ga watan Janairun 2021, a lokacin da magoya bayansa suka mamaye ginin majalisar dokokin ƙasar, a wani yunƙuri na daƙile nasarar zaɓen Joe Biden a 2020.

An yi zargin rasa rayuka kan rikicin, da aka zargi Trump da zuga mutanen.

Ya yi ƙoƙarin rage mahimmancin tarzomar. Daga baya kuma an yanke wa ɗaruruwan masu tarzomar – waɗanda magoya bayansa ne – hukuncin ɗauri a matsayin fursunonin siyasa.

Trump ya ci gaba da cewa da yawa daga cikinsu ”an ɗaure su ne bisa kuskure”, duk da cewa ya amince cewa ”da dama daga cikinsu sun fi ƙarfin zukatansu ne”.

7. Korar mai shigar da ƙara a shari’arsa

Trump ya sha alwashin cewa cikin ”ɗaƙiƙa biyu” na karɓar mulkinsa za kori mai shigar da ƙara na gwamnati da ke jagorantar bincike kan manyan laifuka biyu da ake tuhumarsa da su.

Lauyan na musamman, Jack Smith, ya tuhumi Trump kan zargin yunƙurin sauya sakamakon zaɓen 2020, da kuma zargin riƙe wasu takardun sirrin ƙasa bayan ya bar fadar white house.

Trump ya musanta aikata laifi, sannan ya samu nasarar hana sauraren daya daga cikin waɗanan zarge-zargen kafin zaɓe.

Trump zai koma fadar White House a matsayin mutum na farko da ake tuhuma da aikata wani babban laifi, bayan da aka same shi da laifin ƙarya a takardun kasuwanci a New York.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *