Friday, January 16
Shadow

Gwamnatin Najta tatsi harajin Naira Biliyan 600 daga kamfanonin Facebook, Amazon da Netflix

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta karbi harajin VAT daga kamfanonin Facebook, Netflix da Amazon.

Me baiwa shugaban kasa shawara akan Haraji, Mr Mathew Osanekwune ya bayyana hakan inda yace sun karbi Harajin ne daga kamfanoni na yanar gizo.

Yace gyaran da akawa tsarin karbar Harajin Najeriya ne yasa hukumar karbar haraji ta kasa, Federal Inland Revenue ta fara karbar haraji daga kamfanonin da bana Najeriya ba amma suna da kwastomomi a Najeriya.

Yace tsarin na bisa doka kuma irin shine ana yadda dashi a tsakanin kasa da kasa.

Karanta Wannan  RABO DAGA ALLAH: Wani Mahauci Ya Tsinci Macury A Cikin Saniya Wanda Kudinsa Ya Kusan Naira Milyan Goma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *