Thursday, January 2
Shadow

Gwamnatin Nijar ta kori kamfanonin sadarwa na Faransa

A Jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin sojan kasar ta sanar da korar kamfanonin sadarwa na ƙasar Faransa na Camusat da Aktivko a duk faɗin ƙasar.

Camusat na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a Nijar, da kuma Aktivko wanda ya ƙware wajen samar da makamashi ga turakun sadarwa na wayoyin salula.

Wannan na zuwa ne a loƙacin da hukumomin mulkin sojan Nijar ke ci gaba da korar kamfanonin Faransa daga Nijar a ƙoƙarin raba gari da ita baki daya.

Wata sanarwa da Ministan Sadarwa Sidi Muhammad ya fitar ta ce an haramta wa dukkan ‘yan ƙasa yin aiki tare da kamfanonin, amma babu wani cikakken bayanin dalilin da ya sa gwamnatin ta ɗauki matakin a yanzu.

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yace cikin yaran da gwamnatin Tinubu ta kai kotu jiya akwai 'yan Kano kuma zai dawo dasu gida

Sai dai masu lura da al’amuran yau da kullum a Nijar na cewa matakin ba zai rasa nasaba da tsaron ƙasa ba.

A gefe guda kuma, masu adawa da gwamnatin mulkin sojan na cewa haramcin yunƙuri ne kawai na kafa kamfanin da sojojin ke so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *