Thursday, May 15
Shadow

Gwamnatin taraiya ta umurci WAEC da NECO su koma zana jarrabawa ta na’ura mai ƙwaƙwalwa

Gwamnatin taraiya ta umurci WAEC da NECO su koma zana jarrabawa ta na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Gwamnatin Taraiya ta umurci Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) da Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) da su fara gudanar da dukkan jarabawarsu ta hanyar amfani da Kwamfuta (CBT) daga shekarar 2026.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin da yake sa ido kan jarabawar da ake gudanarwa tare da jami’an JAMB, a Bwari, ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa fiye da dalibai miliyan biyu ne suka yi rajistar jarabawar da ake gudanarwa a fiye da cibiyoyi 800 a fadin kasar nan.

Karanta Wannan  An kama malamar makaranta da laifin yiwa dalibinta me shekaru 17 fyade har ta dauki ciki

Alausa ya bayyana cewa daga watan Nuwamba mai zuwa, WAEC da NECO za su fara gudanar da jarabawarsu ta bangaren tambayoyi (objective) ta hanyar CBT.

A cewarsa, cikakken amfani da CBT zai fara aiki daga watan Mayu ko Yuni na 2026.

Ya ce, “Idan JAMB na iya gudanar da jarabawar CBT ga fiye da dalibai miliyan 2.2 cikin nasara, to WAEC da NECO ma za su iya.”

Ya kara da cewa, “Za mu sa WAEC da NECO su fara gudanar da jarabawar objective a kan CBT. Daga jarabawar shekarar 2026 da za a fara a watan Mayu/Yuni, duka bangaren tambayoyi da rubutu za su kasance a kan CBT gaba daya. Wannan ne zai taimaka wajen kawar da magudin jarabawa.”

Karanta Wannan  A cikin Azumin Watan Ramadana, An kama dan shekaru 35, Abdullaziz Mohammed da yiwa karamar yarinya me shekaru 5 fyade a jihar Adamawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *