Sunday, March 23
Shadow

Nan da ranar 1 ga watan Maris, Gwamnatin Tarayya zata hana motocin dakon man fetur me nauyi hawa titunan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta sanar da fara hana motoci masu daukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 hawa titunan Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris.

Gwamnatin tace zata dauki wannan mataki ne saboda rage yawan hadarurrukan dake faruwa akan titunan Najeriya.

Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin hukumar kula da hadadar man fetur ta (NMDPRA).

Hukumar tace nan da karshen shekarar 2025 ba zasu bar mota me daukar man fetur sama da lita 45,000 ta rika hawa titunan Najeriya ba.

Wakilin hukumar, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da ya wakana a Abuja ranar Laraba.

Ya kara da cewa an samu cimma matsaya tsakanin hukumar tsaron farin kaya ta DSS da hukumar kula da dokokin hanya ta FRSC, da kungiyar direbobi ta NARTO, da kungiyar ma’aikatan man fetur ta NUPENG, da sauran hukumomi akan wannan batu.

Karanta Wannan  Banda mu a cikin wadanda suka saci man fetur daga tankar mai data fadi, Bidiyon karyane ake yadawa>>Inji Hukumar 'yansandan Najeriya

Yace zasu ci gaba da aiki tare dan rika kai man fetur me tsafta ga masu saye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *