
Rahotanni sun bayyana cewa kaso 82 cikin 100 na danyen ma da aka hako a Najeriya, kasashen waje ake sayarmawa inda ake sayarwa da matatun man fetur na cikin gida da sauran kason.
Hakan na zuwane yayin da matatun man fetur din Najeriya irij na Dangote ke kukan rashin wadataccen danyen man da zasu tace.
An samu wadannan alkaluma ne a watanni 3 na farkon shekarar 2025.
Hukumar dake kula da lamarin, NUPRC ta bayyana cewa ganga Miliyan 1.57 ce aka hako a tsakanin watanni 3 din kuma an sayarwa da kasashen waje ganga Miliyan 1.29 inda aka sayarwa da matatun cikin gida ganga 280,000.
Hukumar ta NUPRC tace wannan kaso da take sayarwa da matatun man cikin gida dan ta karfafa su ne, saidai matatar man fetur din Dangote tace tana dogaro da kasar Amurka ne wajan samun danyen man fetur.