
Kungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN ta zargi ma’aikatar kwadago da ma’aikatar harkokin cikin gida da baiwa ‘yan kasar India su kusan dubu 11 damar samun aiki a kamfanin harkar man fetur na Sterling Oil Exploration and Energy Production Company Limited.
Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace wannan aiki da aka baiwa Indiyawan aikin ‘yan Najeriya ne.
Dan haka ya bukaci a kwace aikin a baiwa ‘yan Najeriya su kuma indiyawan a mayar dasu kasarsu.
Yace idan ba’a yi hakan ba, zasu dakatar da ayyukansu sannan zasu shiga gagarumin yajin aiki.
Yace ba zai yiyu ana kukan babu aiki a kasa ba a rika dauko ‘yan wata kasa da yawa haka ana basu aikin da ya kamata ‘yan kasa suke yi ba.
Yace dole gwamnati ta zaba ko dai ta goyi bayan ‘yan Najeriyar ko kuma ta goyi bayan indiyawan.