Monday, April 21
Shadow

Bayan da ya koma APC, shugaba Tinubu ya baiwa Sanata Shehu Sani mukamin Jakada

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fitar da sunayen mutanen da zai baiwa aikin jakadancin Najeriya zuwa kasashen waje.

Tuni dai aka nemi wadanda sunayensu ya fita cewa su je ofishin DSS na kusa dasu dan a musu bincike kan tsaro sannan su bayar da bayanai kan ayyukan da suka taba yi a baya.

Wata majiya me karfi ta bayyanawa jaridar Vanguard cewa akwai sunan Shehu Sani wanda bai dade da komawa jam’iyyar APC ba cikin wadanda aka baiwa mukamin sanatan.

Sannan akwai tsaffin gwamnonin jihohin inyamurai watau Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu.

Sannan majiyar tace akwai sunan Femi Fani Kayode sannan kuma akwai sunan Reno Omokri.

Karanta Wannan  Peter Obi ya kai wa gwamnan Bauchi ziyarar tuntuɓa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *