
Gwamnatin tarayya ta bayar da ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu dan yin bikin ranar ma’aikata.
Gwamnatin tace akwai bukatar zaman lafiya dan ci gaban masana’antu da tattalin arziki.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da haka a madadin gwamnatin tarayya.