Wednesday, January 14
Shadow

Gwamnatin tarayya ta dauki wasu Amurkawa aiki dan su rika tabbatarwa da Gwamnatin Amurka cewa tana baiwa Kiristoci kariya

Gwamnatin tarayya ta dauki wasu Amurkawa aiki inda zata biyasu dala Miliyan $9 dan su rika gayawa Gwamnatin kasar Amurkar kokarin da suke yi na baiwa Kiristocin Najeriya kariya.

Kafar TheCable tace sunan kamfanin Amurkar da zaiwa Gwamnatin Najeriya aiki DCI Group, shi wannan kamfanin aikinsa shine ya rika taimakawa duk wani me son yin hulda da kasar ta Amurka kaiwa Gwamnatin bayani.

Dan hakane Gwamnatin tarayya ta daukeshi aiki ya rika kaiwa Gwamnatin tarayya bayanai kan kokarin da take na baiwa Kiristocin Najeriya kariya.

Hakan na zuwane yayin sa kasar Amurka ta zargi Gwamnatin Najeriya da cewa, tana bari ana Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya.

Karanta Wannan  Bidiyo: Ba haka ake aiki ba, wannan zubar da mutunci ne>>Hukumar 'yansandan Najeriya ta yi Allah wadai da yanda wasu 'yansanda suka yiwa wata jarumar fina-finan kudu da ta yi shigar banza rakiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *