A ranar Laraba, Gwamnatin tarayya ta janye zarge-zarge 3 na ta’ddanci da takewa shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo.
Tun a watan Janairu ne dai sojoji ke tsare da Bodejo bisa wannan zargi inda suka ki bayar da belinsa.
Saidai a ranar Laraba da Ministan Shari’a ya je gabatar da Zarge-Zargen da akewa Bodejo dan ci gaba da shari’a, sai ya ce gwamnati ta janye karar data shigar akanshi.
Wannan lamari dai ya zowa mutane da mamaki ganin cewa a baya gwamnatin ko beli ta ki yadda ta bayar da Bodejon.
Ana dai zargin Bidejo ne da kafa wata kungiyar Funali wadda ake zargin ta ta’ddanci ce da kuma basu makamai da sauran kayan aiki.