
Gwamnatin tarayya ta kayyade shekaru 12 a matsayin shekarun shiga ajin karamar sakandare na JSS1.
Hakan na kunshene a bayanan da gwamnati ta fitar kan yanda makarantun kudi zasu riga gudanar da harkar ilimi.
Sanarwar tace yaro sai ya kai shekara 3 sannan za’a sakashi a ajin Nursery 1
Sannan idan ya kai shekaru 4 a sakashi a ajin Nursery 2.
Gwamnati tace kamin yaro ya fara ajin farko na primary watau Primary one sai ya kai shekaru 6.
Dan haka kowane yaro sai ya kai shekaru 6 yana karatun Primary daidai lokacin da zai kammala Primary, ya zamana yana da shekaru 12.
Dokar tace a daidai lokacin da yaro zai kammala sakandare zai kasance yana da shekaru 18 kenan.