Gwamnatin tarayya ta warewa kamfanin kera makamai na sojojin Najaria, DICONs Naira N7,940,323,192.
Kamfanin wanda aka kirkira a shekarar 1963 a samar dashine dan ya rika kerawa sojojin Najaria makamai.
Hakanan dukkan gwamnatocin da aka yi a Najeriya na warewa kamfanin makudan kudade dan ingantashi, saidai har yanzu baya yin wani aikin azo a gani.
Duk da kasancewar kamfanin, Har yanzu Najeriya na siyo mafi yawancin makamanta da ake amfani dasu ne daga kasashen waje.