Thursday, June 19
Shadow

Gwamnatin tarayya tace za’a rika koyar da sana’o’in Gyaran fanfo, Aski, Gyaran waya, kwalliyar mata da sauransu a makarantun b0k0

Gwamnatin tarayya tace an saka sana’o’in Aski, Gyaran waya, gyaran fanfo, kwalliyar mata, Gyaran waya da sauransu cikin abubuwan da za’a rika koyarwa a makarantun boko.

Za’a rika koyar da wadannan sana’o’i ne a makarantun firamare zuwa makarantun karamar sakandare.

Wannan ya biyo bayan garambawul da akawa bangaren ilimi.

Hukumar wayar da kai ta kasa, NOA ta ce an saka wadannan sana’o’i cikin karatu ne dan koyawa dalibai hanyar dogaro da kai.

Sauran sana’o’in da za’a rika koyarwa sun hada da noma, kiwon kaji, gini, saka tayil, saka POP, da dai sauransu.

Karanta Wannan  Haduwar Mawakiyar Najeriya, Ayra Starr da shahararriyar me yin fina-finan bàtsà Mìa Khàlìfà ya jawo cece-kuce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *