
Gwamnatin tarayya ta sanar da aniyarta ta baiwa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa kyautar kidade da gidaje da motoci.
Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar kananan da matsakaitan masana’antu Temitola Adekunle-Johnson ne ya bayyana hakan ranar Litinin.
Yace zasu bude shafin yin rijista nan da 7 ga watan Maris inda za’a kulle yin rijistar ranar 7 ga watan Afrilu.
Yace zasu duba irin gudummawar da kasuwanci ya kawowa Najeriya kamin su zabeshi.