Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Tarayya zata bayar da bashin Naira Dubu Biyar ga ‘yan Kasuwa da Manoma, Ji yanda zaku samu

Gwamnatin tarayya zata fara bayar da bashin GEEP ga manoma da kananan ‘yan kasuwa.

Shugaban tsarin Hamza Ibrahim Baba ne ya bayyana haka a Kaduna yayin ganawa da wakilan ‘yan kasuwar da manoma a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa, za’a bayar da bashine ba tare da ruwa ko jingina ba.

Yace kuma bashin daga Naira dubu biyar ne har zuwa Naira dubu dari.

Yace kuma za’a bada tazarar watanni 6 kamin a faa biyan bashin.

Yace za’a fara bayar da bashin kamin karshen shekarar 2025 da muke ciki a dukkan fadin Najeriya.

Yace bashin zai taimakawa manoman da ‘yan kasuwar sayen kayan amfaninsu.

Karanta Wannan  Ji bayani dalla-dalla: Shugaba Tinubu ne yacewa Ganduje ya sauka daga shugabancin APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *