
Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin gyarawa ma’aikatan ta tsarin kiwon lafiyarsu.
Gwamnatin tace hakan ya zama dole musamman lura da hauhawar farashin magunguna.
Gwamnatin ta bayyana hakane a yayin gwaji kyauta da kawa ma’aikatan a lokacin bikin satin ma’aikata a Abuja.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mrs Didi Walson-Jack ce ta bayyana hakan a wajan inda tace kula da lafiyar ma’aikatan na da muhimmanci musamman lura da muhimmancin aikin da suke.
Tace tsarin da ake kai a yanzu ya zama tsohon yayi yana da kyau a sake dubawa dan sabuntashi.