Monday, December 16
Shadow

Gwamnatin Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a shekara daya da ta yi tana mulki, ko me aka yi da kudin?

Masana sun bayyana damuwa game da yawan bashin da gwamnatin tarayya ta ciwo a shekara daya data gabata.

Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a hannun ‘yan Najeriya.

Hakan na nuna cewa, yawan bashin da gwamnatin Tinubu ta ciwo ya fi wanda Gwamnatin Buhari ta ciwo a shekararta ta karshe akan mulki da kaso 117.

Masana sun bayyana damuwar cewa hakan zai iya kawo karuwar hauhawar farashin kayan abinci da kara kudin ruwa na karbar bashi.

Karanta Wannan  Bai kamata Tinubu ya soki Gwamnatin Buhari ba saboda cewa yayi zai dora daga inda Buhari ya tsaya>>Buba Galadima

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *