A cikin watanni 16 da suka gabata, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ranto jimullar kudin da suka kai Dala Biliyan 6.45 daga bankin Duniya.
Bayanai sun nuna an ranto kudadenne dan dan gudanar da ayyuka daban-daban a fadin kasarnan. Kuma ana tsammanin nan gaba gwamnatin zata sake ranto wasu kudaden.
Da yawan ‘yan Najeriya dai na ganin basukan da gwamnati ke ciyowa basu da wani tasiri sosai musamman ganin yanda gwamnatocin baya ke ciwo bashi amma babu abinda ke canjawa.
Lamarin ciwo bashi dai ya zama kamar gasa tsakanin gwamnatocin Najeriya inda duk gwamnatin data hau mulki sai ta ciwo bashi a wasu lokutan ma wanda yafi na gwamnatin data gabata.
Abin jira a gani dai shine ko wannan gwamnati zata sha banban da sauran gwamnatocin?