Saturday, May 24
Shadow

Gwamnatin Zamfara ta mayar da dabbobi 3,000 da aka sace ga asalin masu su

Gwamnatin Zamfara ta mayar da dabbobi 3,000 da aka sace ga asalin masu su.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta mayar da dabbobi 3,000 da jami’an tsaro suka kwato daga hannun barayin shanu ga asalin masu su cikin wata 15 da suka gabata.

Shugaban kwamitin tantance dabbobin da aka kwato, Sheikh Sa’idu Maikwano, ne ya bayyana hakan a wani taro da sakataren gwamnatin jihar Abubakar Nakwada.

Taron dai na da nufin tsara sabbin dabaru da hanyoyi masu inganci don tabbatar da nasarar aikin kwamitin, musamman yanzu da jami’an tsaro ke samun nasarori sakamakon karin hare-haren da suke kaiwa a fadin jihar.

Dabbobin da aka mayar sun hada da shanu, tumaki da awaki da sauransu.

Karanta Wannan  Hotunan Sabon Jirgin Saman Shugaban Kasa Bola Tinubu

Shugaban kwamitin ya yaba wa Sakataren Gwamnatin jihar, kan yadda yake sa ido yadda ya kamata a kan aikin kwamitin.

Haka kuma, ya gode wa Gwamna Dauda Lawal bisa goyon bayan da ya bayar wanda ya taimaka wajen cimma nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *