
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Gwamnatinsa ta baiwa mutane 100,000 bashi.
Sannan akwai wasu 400,000 da suke kan layi suma za’a basu bashin.
Akwai tsare-tsaren bashi da yawa da Gwamnatin Tinubu ta kawo saidai da yawan ‘yan Najeriya na kokawa da cewa basa samu ko da sun nema.