
An gano gawar wani dansandan Najeriya a dakin otal dake Uzum Estate, Oyeyemi Akute jihar Ogun.
Sunan Otal din Super G Royal Hotel sannan sunan dansandan da aka gawarsa, Inspector Haruna Mohammed.
Saidai matar da suka shiga dakin otal din da ita ta tsere ba’a san inda ta yi ba.
Rahoton jaridar thenation ya bayyana cewa, dansandan ya shiga otal din da matar ranar February 15, 2025 da misalin karfe 1 na dare.
Ganin karshe da akawa matar da suka shiga dakin da ita shine da misalin karfe shida na safe inda ta bukaci a bata ruwan sha.
Manajar otal din wadda macece ta fara ganin gawar dansandan inda tuni aka tafi da ita ofishin ‘yansandan dan gudanar da bincike.
Kakakin ‘yansandan jihar, CSP Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun gano gawar babu wata alamar ciwo a jikinta amma suna kan ci gaba da bincike.
Tuni aka kai gawar dansandan zuwa Mutuware inda ana kokarin gano dansandan gaskene ko kuwa duk da an ganshi da kayan ‘yansanda.