
Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala ya bayyana cewa, Gwamnonin Najeriya na jin dadin cire tallafin man fetur da aka yi.
Yace a yanzu babu Gwamnan da baya iya biyan ma’aikatan jiharsa Albashi.
Yace maimakon a baya wanda gwamnoni kusan sama da 20 ne basa iya biyan Albashi.
Daniel Bwala ya bayyana hakane a yayin zantawar da aka yi dashi a gidan Talabijin na chan TV.
Ya kuma ce gwamnonin a yanzu suna samun kudaden gudanar da ayyuka a jihohinsu ba kamar a baya ba.