Sunday, May 4
Shadow

Gwamnonin APC sun kai wa Muhammadu Buhari ziyara

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya karkashin jagorancin shugabanta gwamnan Imo Sanata Hope Uzodinma, ta kai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyarar ban girma a gidansa da ke Kaduna.

Bayan shugaban kungiyar, sauran gwamnonin da suke cikin tawagar ma su ziyarar sun hada da gwamnan Kaduna da na Gombe da Kwara da Nasarawa da Ebonyi da Kebbi da Edo da Kogi da Ondo da Ekiti da kuma Benue.

Sauran ‘yan tawagar sun hadar da mataimakin gwamnan Jigawa da ministan kasafin kudi da tsare-tsare.

Karanta Wannan  2027: Nan da watanni 6 yankin Arewacin Najeriya zai bayyana matsayar sa kan zaben shugaban kasa - Hakeem Baba-Ahmed

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *