Monday, April 21
Shadow

Saudiyya ta ayyana ranar da masu aikin Umrah za su fice daga kasar

Ma’aikatar aikin Hajj da Umrah ta Saudi Arabiya ta kebe ranar 1 ga watan Dhul Qada, wadda ta zo dai-dai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ya shiga kasar domin yin Umrah ya fice.

Ma’aikatar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa.

Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi dai-dai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita.

Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har ya wuce lokacin da kebe, to ko shakka babu ya saba ka’ida sannan kuma zai fuskanci hukunci.

Karanta Wannan  Dan Fim Din Kudu ya bayar da labarin yanda abokan aikinsa mata 3 suka masa fyàdè a yayin da suke wani otal daukar fim

Daga nan ta bukaci mutane da ma kamfanonin da ke shirya zuwa aikin Umrah da su kiyaye da wadannan lokuta da aka kayyade.

Ma’aikatar ta yi gargadin cewa duk wani jinkiri na barin mutane kasar za a dauke shi kamar karya doka.

Ta ce duk kamfanin da aka samu da kin bayyana mutanen da suka ki koma wa kasashensu to za a ci tararsu riyar dubu 100.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *